Ƙamus
na Kalmomin Kasuwar Jari

Mai Ciniki da Kuɗin Kansa
Mai shiga tsakani na kuɗi wanda ke saye ko sayar da takardun jari da kuɗin kansa, ba a madadin abokan ciniki kamar dillalan hannayen jari ba. Saboda haka yana aiki a matsayin mai ma’amalar da kansa. Yana sake sayar wa abokan ciniki da rarar da aka amince da ita sama da farashin ciniki. Wannan rara ce kuɗinsa domin ba ya karɓar kwamishan.
Mai Tsammanin Faɗuwar Farashi
Wanda yake tsammanin darajar takardun jari ko kayayyaki gaba ɗaya, ko takamaiman takarda ko kaya da ake ciniki a musaya ko wajen musaya, za ta ragu.
Memba Mai Ciniki
Memban musayar hannayen jari mai izinin saye da sayar da takardun jari a madadin jama’a ko da kuɗin kansa.